Tabdijam: Yadda Uba Ya Gwada Diyarsa Don Gano Ko Tana Sana’ar Gidan Magajiya a Makaranta
Wani magidanci ɗan Najeriya ya gwangwaje ɗiyar sa da kyautar maƙudan kuɗaɗe bayan yayi mata gwajin kwantawa da wani saboda N300k.
Da yake magana da Shuga Plum, wata mai yin bidiyon gwaji, mutumin yace yana ganin yadda maza ke ɗaukar ƴanmata sannan yana son ya san halayyar ɗiyar sa a makaranta. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Dimokuradiyya
Home Al'ajabi
Tabdijam: Yadda Uba Ya Gwada Diyarsa Don Gano Ko Tana Sana’ar Gidan Magajiya a Makaranta
Sharif Addubawi by Sharif Addubawi April 6, 2023 Reading Time: 2 mins read
Tabdijam: Yadda Uba Ya Gwada Diyarsa Don Gano Ko Tana Sana’ar Gidan Magajiya a Makaranta
51
SHARES
Wani magidanci ɗan Najeriya ya gwangwaje ɗiyar sa da kyautar maƙudan kuɗaɗe bayan yayi mata gwajin kwantawa da wani saboda N300k.
Da yake magana da Shuga Plum, wata mai yin bidiyon gwaji, mutumin yace yana ganin yadda maza ke ɗaukar ƴanmata sannan yana son ya san halayyar ɗiyar sa a makaranta. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Majalisar Wakilai Ta Dakatar Da NDDC Daga Sakin Naira Biliyan 15 Agaji Ga FG
Yaje wajen da aka shirya yin gwajin sannan sai ya ɓoye. Ga mamakin sa sai ya ɗiyar tasa mai suna Chidinma ta zo wajen sannan tayi watsi da tatin da akai mata inda ta bayyana cewa bata taɓa kwanciya da wani namiji ba.
Cikin farin ciki mahaifin ya fito daga ɓoyon da yayi sannan ya riƙa yabon ɗiyar tasa da karfi.
A nan take a wajen, yaba ɗiyar tasa kyautar naira miliyan ɗaya (N1m), alƙawarin kai ta Canada da kyautar mota. Cikin farin ciki suka rungume juna.
Bidiyon ya ɗauki hankula sosai, inda mutane da dama suka yi ta sharhi a kansa.
Ku kalli bidiyon a nan
Ha kaɗan daga cikin waɗanda Dimokuraɗiyya ta tattaro:
@Idris Bawa ya rubuta:
“Amen. Ƴar albarka ce
Allah ya kare ta ya ƙara ɗaukaka ta zama abin alfahari ga al’umma.”
@Big Boy ya rubuta:
Shuga plum yanzu an san ki sosai ta iya yiwuwa ba za su faɗa tarkon wasan da kike shiryawa ba. Lokaci na gaba ki bari wani yayi mu ga yaya zata kasance.”
@enenduelcee ya rubuta:
“Wannan shine ba’a mafi kyau da na taɓa gani. Na ji daɗi wa mahaifin da ɗiyar sa da iyalan su. Wannan mace auren ce. Ta samu tarbiyya mai kyau.”

Comments
Post a Comment