Hasashe mai daukar hankali: Musulmai za su azumci Ramadana sau biyu a 2030
Hasashe mai daukar hankali: Musulmai za su azumci Ramadana sau biyu a 2030
Wani rahoton hasashe da jaridun kasashen Larabawa suka fitar ya bayyana yadda za a samu sauyin yin azumin Ramadana Wannan sauyi zai faru ne bisa sauyin yanayi kamar yadda masana ilimin taurari suka hango inji rahoton A shekarar 2030, ana kyautata zaton za a yi azumin Ramadana sau biyu a cikinsa, bisa hangen masana ilimin taurari
Dubai, Daular Larabawa - Jaridar Arab News ta tattaro cewa, musulmai za su yi azumin Ramadana sau biyu a shekara ta 2030, kamar yadda wasu masana ilmin taurari suka yi hasashen. Masana sun ce watan azumi zai shigo sau biyu a wannan shekara ta 2030, na farko a watan Janairu, sannan kuma a karshen watan Disamba, lamarin da ya taba faruwa a shekarar 1997.


Comments
Post a Comment