An gurfanar da shahararren mawaƙin APCn nan Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara), a gaban babbar kotun shari'ar addinin musulinci dake zaman ta a unguwar Rijiyar Zaki Kano, ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Halhaltul Khuza'i Zakariya.

 ANA WATA GA WATA: Rarara Ya Shiga Tangal-tangal Ɗin Wasan Ƴar Ɓuya Da Jami'an Kotu Kan Bashi Sammacin Tuhumar Sama Da Naira Miliyan Goma



An gurfanar da shahararren mawaƙin  APCn nan Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara), a gaban babbar kotun shari'ar addinin musulinci dake zaman ta a unguwar Rijiyar Zaki Kano, ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Halhaltul Khuza'i Zakariya.


Tun da fari wani mai suna Muhammad Ma'aji ne ya maka Rarara a gaban kotun kan wasu kuɗaɗen sa Naira Miliyan ₦10.3m da suka ƙulla wata harka a watannin da suka gabata.


Mai ƙarar ya shaida wa kotun cewa, bashi da wani zaɓi dan ya ƙarɓi haƙƙinsa sai ta fannin shari'a kamar yadda kowa yake da ƴan cin shigar da ƙara kan hanashi haƙƙinsa.


Muhammad Ma'aji ya ƙara da cewa ya bi matakin sulhu da wanda yake ƙara dan ya bashi kuɗin sa tunda dai harkar bata yiwu ba kuma yaƙi bashi kuɗinsa.


Kakakin manyan kotunan shari'ar Addinin musulinci na jahar Kano Muzammil Ado Fagge, ya bayyana cewa, za a fara sauraran ƙarar a ranar 11 ga watan Afrilun 2023.


"Wannan ƙara ce wadda Muhammad Ma'aji ya shigar da Rarara mawaƙin jam'iyyar APC kuma ƙara ce wadda akwai mu'amulla da shi har ta naira miliyan 10 kuma ya yi, ya bashi ƙuɗin amma yaƙi." Inji Muzammil A. Fagge


Shafin yanar gizo na Oddity24 ya ruwaito cewa kakakin manyan kotunan shari'ar addinin muslincin na jahar Kano, ya ce sun yi amfani da doka da Oda ta 9 2021 da ta yi magana cewa idan aka nemi mutum dan a bashi sammaci ba aganshi ba to za a iya yin amfani da shafukan sada zumunta dan sanar da shi ko kuma a liƙa masa a gidan sa.


"Shi wannan Mawaƙin sai wasan ɓuya yake yi da jami'in mu dan ya bashi sammacin amma yaƙi yadda su haɗu, shi yasa muka nemi mai unguwarsa da kuma shaidu muka liƙa masa a gidan sa dake Zoo Road.

Comments

Popular posts from this blog

Yadda zaku hada maganin karin Kuzari da Karfi a lokacin saduwa da iyali 👇👇👇👇

Sahihin maganin kwanciyar Nono wanda zai sa Nonuwan Mace su ciko suyi kyau 👇👇👇👇